Ba a yi zabe a kananan hukumomin Kaura da Jaba ba sannan har yanzu ba a sanar da zabukan Kajuru, Kagarko da Kaduna ta Kudu ba.
Ga sakamakon kamar yadda Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ya sanar:
1. Kubau – Sabo Aminu na jam’iyyar APC ya sami kuri’u 46,535, Umar Abdullahi na jami’yyar PDP ya sami kuri’u 13,398.
2. Giwa – Abu Shehu Lawal Giwa na jami’yyar APC ya sami kuri’u 57,005, Bello Shehu Kago na jami’yyar PDP ya sami kuri’u 2,673
3. Ikara – Salihu Sadiq na jami’iyyar APC ya sami kuri’u 42,312, Abdullahi Aliyu na PDP ya sami kuri’u 9,248.
4. Lere – Abubakar Buba ya sami kuri’u 92,854, Jumare Tanimu na PDP ya sami kuri’u 16,231.
5. Sabon Gari – Mohammed Ibrahim Usman na APC ya sami kuri’u 20,576, Suleiman Ibrahim Gambo na PDP ya sami kuri’u 9,580.
6. Kaduna ta Arewa – Saleh Shuaibu na APC ya sami kuri’u 168,572, Muhammad Sabo Babayaro na PDP ya sami kuri’u 12,467 sannan dan takaran jami’yyar PRP ya sami kuri’u 4,956.
7. Kudan – Shu’aibu Bawa Jaja na APC ya sami kuri’u 72,021, Kabiru Isiaku na PDP ya sami kuri’u 3,394.
8. Igabi – Jabir Khamis na APC ya sami kuri’u 47,630, Abubakar Abubakar na PDP ya sami kuri’u 2,449.
9. Soba – Mohammed Mahmud Aliyu na APC ya sami kuri’u 40,903, Muhammad Surajo Tukur na PDP ya sami kuri’u 13,835.
10. Zaria – Aliyu Idris Ibrahim na APC ya sami kuri’u 42,859, Yusuf Namadi na PDP ya sami kuri’u 16,033.
11. Makarfi – Kabiru Musa Meyere na APC ya sami kuri’u 25,199, Ibrahim Isyaku na PDP ya sami kuri’u 13,088.
12. Kauru – Shuaibu Goma na jami’yyar PDP ya sami kuri’u 24,393, Bashir Tanko daga jami’yyar APC ya sami kuri’u 21,564.
13. Sanga – Samuel Shamaki na PDP ya sami kuri’u 20,843, Charles Danladi na APC ya sami kuri’u 19,757.
14. Kachia – Peter Agite na PDP ya sami kuri’u 42,242, Peter Dan- Baki na APC ya sami kuri ‘u 33,817
15. Zangon Kataf – Elias Maza na PDP ya sami kuri’u 55,643, John Hassan ya sami kuri’u 31,514
16. Jema’a Peter Averik na PDP ya sami kuri’u 45,361, Cecelia Musa na APC ta sami kuri’u 25,973.
17 – Birnin Gwari – APC ce ta lashe zabe a Birnin Gwari.