‘Yan tireda masu saida gwanjo a garin Mararraba da ke hanyar Abuja zuwa Keffi, sun nuna damuwa game da wa’adin tashi daga inda suke kasuwancin su.
Gwamnatin jihar Nasarawa ta ba su wa’adin daga ranar Litinin, 14 Ga Mayu, ba son ganin ko daya daga cikin su a wurin.
Shugaban Kwamitin Tafi da Gidan ka kan tayar da masu saida gwanjon ne ya bada wa’adin a wata ganawa da ya yi da kungiyar ‘yan tireda da kuma ta masu motocin sufuri.
Shugaban Kungiyar masu saida kayan gwanjo na wurin, Sulaiman Hassan, ya bayyana wa Kamfanin Dillancin Labarai cewa an ba su wa’adin cewa a yau 15 Ga Mayu ba a son ganin jowa daga cikin su.
Ya ce an ba su sanarwar cewa masu kasa kaya a bakin titi na haddasa cinkoson jama’a da motoci a kan titi. Dalilin kenan ake son a tayar da su daga inda suke.
Sai dai kuma sun nuna damuwar cewa an yi musu ba daidai ba, domin an ba su wa’adi na kurarren lokaci, ba tare da an ba su isassshen lokacin shiryawa ba.
An nuna musu cewa za su koma ne a sabuwar kasuwar da Shugaba Muhammadu Buhari Ya bude kwanan baya, “Inda ake so mu koma, wuri ne kare-kukan-ka, babu jama’a kewaye ko a kusa da wurin. Ta ina masu sha’awar sayen mu za su shigo kasuwar su sayi kayan mu? Wa ya san ma mu na ciki?
Inda fa suke so mu koma, fili ne makeke kamar filin kwallo, babu gini ko rumfuna, babu shaguna, kai babu ma inda za mu fake ruwa, ko mu adana kayan mu don kada su jike, idan ruwa ya goce. Ta ya za mu kira wurin kasuwa?
Hassan ya roki gwamnati ta kara musu wa’adi domin a samar musu wurin da ya fi dacewa a maida su, amma ba inda aka yi niyyar maida su yanzu ba.