Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kuranta kan sa da jam’iyyar sa ta APC cewa nasarorin da gwamnatin sa ta samu a tsawon mulkin ta na shekaru uku, PDP ba ta iya samun haka ba a tsawon shekaru 16 da tayi ta na mulkin Najeriya.
Buhari ya bayyana haka ne a ziyarar aiki da ya kai Jihar Jigawa ranar litinin.
A fadar mai martaba Sarkin Hadejia, Buhari ya godewa mutanen Hadejia musamman ga irin maraba da suka yi masa.
Ya ce daga yanzu gwamnatin sa zata maida hankali wajen kawo ayyukan ci gaba a wannan masarauta.
Da yake bayani, Sarkin Hadejia, Adamu Maje, ya yi wa Shugaba Buhari fatan alkhairi da goyon baya ga gwamnatin sa.
Daga Karshe an yi wa Buhari addu’a ta musamman domin samun karin Lafiya.
Kafin nan shugaba Buhari ya kaddamar da ci gaba da fadada dam din Auyo dake masarautar.
A garin Dutse Buhari ya ziyarci fadar Sarkin Dutse. A nan ma Shugaban Kasa ya yi wa mutanen garin alkawarin ci gaba kawo musu ababen more rayuwa.
Shi kuwa sarkin Dutse rokon shugaba Buhari yayi ya taimaka a maida cibiyar noman Dabino zuwa jami’an gwamnatin tarayya da ke Jihar.