Tsohon Shugaban kasa na mulkin soja, Janar Yakubu Gowon, ya bayyana cewa mai yiwuwa matsayin da ya tsinci kan sa bayan an yi masa juyin mulki cikin 1975, shi ne ya sauya tunanin shugabannin Najeriya dangane da cin hanci da rashawa.
Da ya ke tuna abin da ya faru a 1975, ya ce a lokacin da aka cire shi daga mulki, ba shi da komai sai albashin sa.
Gowon ya na jawabi ne a Taron Kasashen Afrika Renon Ingila kan cin hanci da rashawa, a Abuja, inda har ya yi barkwancin cewa, a lokacin da aka hambarar da shi, bai yi tanadin komai a rayuwar sa ba.
Ya ci gaba da cewa, bayan an hambarar da shi, wasu daga cikin ma’aikatan sa ne da ya tafi taron Kasashen Afrika da su, suka ji kan sa, su ka ba shi sauran kudin guzirin su, domin ya samu dan na cefane kafin wani lokaci.
A nan ne ya ce watakila mawuyacin halin da ya tsinci kan sa ne bayan an hambarar da shi, ya sa idan shugabanni sun hau mulki, sai su yi gagarimin shirin yadda rayuwar su za ta kasance, bayan sun bar mulki.
Daga nan sai ya kara yin nuni da cewa jami’an gwamnatin sa ba su raja’a wajen harkallar cin hanci ba.
“Duk abin da kasar nan ta mallaka a lokacin, na Najeriya ne, hakkin ta ne, na jama’ar ta ne, kuma babu dalilin taba komai a ciki.”
Ya kuma yi takaicin yadda wasu shugabannin kasar nan suka bata wa sauran shugabannin suna, har ake yi musu jam’un kudin goro, ana ce musu duk barayi ne.
Discussion about this post