Shugaban hukumar inshoran kiwon lafiya na jihar Bayelsa Zuoboemi Agadah ya bayyana cewa gwamnati ta saka ma’aitakan gwamnati da suka kai 80,000 shirin inshoran kiwon lafiya ta kasa.
Ya fadi haka a Yenagoa da yake sa hannu a takardar yarjejeniya tsakanin gwamnatin jihar da asibitocin dake shirin inshorar lafiya ta kasa (HMO) da Kungiyar ‘United Healthcare International’.
Ya ce ma’aikatan jihar sun fara amfana ne da shirin inshorar lafiya ta kasa ne tun daga watan Yunin 2017 sannan zata saka ma’aikatan da ba na gwamanti cikin shirin nan ba da dadewa ba.
Agadah ya ce wannan mataki da suke dauka ya haifar musu da kyawawan sakamako a jihar.