SHAYE-SHAYEN KODIN: Za mu taimaka wa gwamnatin Najeriya – Kamfanin Emzor

0

Jami’ar kamfanin sarrafa magunguna na ‘Emzor’ Stella Okoli ta bayyana cewa kamfani Emzor a shirye take ta mara wa gwamnati baya don kula da wadanda ke fama da matsalolin da shaye-shayen miyagun kwayoyi ya haddasa musu a jiki.

Ta fadi haka ne ranar Lahadi wa manema labarai a jihar Legas.

Idan ba a manta ba a makon da ta gabata ne hukumar NAFDAC ta rufe sashen sarrafa magungunan na kamfanin ‘Emzor’ dake Legas sanadiyyar a dalilin sarrafa wa da siyar da maganin tari mai dauke da Kodin da kamfanin ke yi.

Hukumar NAFDAC ta dauki wannan mataki ne bayan bidiyon da BBC game da maganin da illar da yake yi wa matasan Najeriya.

Hakan ya sa gwamnati ta dauki matakin hana siyar wa da sarrafa wannan magani domin ceto rayukan matasan kasar nan..

A karshe shugaban kamfanin Uzoma Ezeoke ta bayyana cewa bayan hukuma ta tabbatar cewa kamfaninsu bata da hannu wajen sarrafa wa da siyar da wannan magani ne ta yarda ta ci gaba da aikin ta.

” Mu kuma a kamfanin mu, za mu ci gaba da aiki tukuru wajen ganin mun taimaka wa wa gwamnati don kawar da wannan matsala da yake neman ya kar matasan mu.”

Share.

game da Author