Hussaini da Nura sun kashe kanin su Mahmood a dalilin zargin ya sace musu waya

0

Rundunar ‘yan sandan jihar Neja ta bayyana cewa ta nan neman wasu ‘yan uwa biyu da ake zargin sun kashe kanin su a dalilin zargin wai ya sace musu waya.

Mahmood Adamu kanin Nura Adamu ne da Hussaini Adamu kamar yadda ‘yan sandan suka sanar wa manema labarai.

Nura da Hussaini sun zargi kanin su Mahmood cewa ya sace wa dayan su waya, daga nan suka haushi da duka. Da yake ya zo kan karewar kwana, Mahmood ya rasu nan take.

Kakakin ‘yan sandan Muhammad Abubakar yace ko da yake duk sun gudu bayan aikta wannan mummunar aiki, ‘yan sanda sun fantsama neman su.

” Ina tabbatar muku cewa tabbas zamu kama su kuma za su fuskanci hukunci.” Inji Abubakar.

Share.

game da Author