Jami’ar hukumar adana jini na kasa (NBTS) Jane Akubuiro ta koka kan rashin samun isassun mutane masu bada gudunmawar jini kyauta da hukumar ke fama da shi.
A bayanan da ta yi Akbbuiro ta bayyan cewa a rana kamata ya yi hukumar ta a sami akalla mutane 30 amma da kyar ake amun biyar da suke zuwa.
Ta ce wannan matsalar da hukumar ke fama da shi na da nasaba ne da rashin wayar wa mutane kai game da amfanun bada gudunmawar jini.
‘‘Mafi yawan mutane na tunani cewa akan samu matsaloli kamar su rashin samun isasshen jini a jiki idan mutum ya bada gudunmawar jininsa. Amma ina tabbatar musu da cewa mutum na bada jininsa cikin kankanen lokaci bargon jikinsa ke fara aikin mayar wa jiki yawan wannan jini da ya fitar ko kuma ya bada’’.
Discussion about this post