Ministan Kwadago, Chris Ngege, ya bayyana cewa ya na da kyakkyawan yakinin cewa ‘yan Najeriya za su sake zaben Shugaba Muhammadu Buhari a zaben shugaban kasa na 2019.
Ngige ya yi wannan bayanin ne a garin Ojoto, cikin Karamar Hukumar Idemili ta Kudu, yayin da ya ke jawabi ga zababbun shugabannin jam’iyyar karamar hukumar.
Ministan ya ce Buhari ya yi kokarin da ya kamata a sake zaben sa domin ya ci gaba a zangon shugabancin sa na biyu.
A kan haka ne ya ce ko shakka babu, Buhari zai sake yi gaggarimar nasara a zaben 2019.
Ngige ya ce APC za ta tsaya takarar dukkann mukamai, don haka duk magoya bayan jam’iyyar su tabbatar ta samu nasarar kashi 70 cikin 100 kuri’un da za a jefa a jihar.
Daga nan sai ya yaba da irin yadda jam’iyyar APC ta gudanar da zaben ta a dukkan fadinn kananan hukumomin jihar su 26.