Amarya ta gudu bayan miji ya kasa hada kayan lefe

0

Jami’an ‘yan sanda a Suleja, Jihar Neja sun cafke iyayen wata amarya bayan ta ki tarewa a gidan miji, da aka daura musu aure.

Wani mai suna Shuaibu Dauda ne ya kai karar, ya ce sa’o’i kadan bayan daura aure, an nemi amarya amma aka rasa inda ta ke.

Dauda shi ne angon kuma shi ya kai karar surukan na sa, su kuma ‘yan sanda su ka damko su.

Babban jami’in ‘yan sanda na Kaduna Road, Aliyu Lawal, shi ne ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai wannan bayani.

Ya shaida masa cewa yayin da mata ‘yan daukar amarya suka rangada kwalliya suka nufi gidan iyayen amarya, sai suka nemi amarya amma ba amo, kuma babu labari.

Sufeto Lawal ya ce ganin yadda iyayen amarya suka rika jan-kafa wajen fito wa iyayen ango da amarya, hakan ya kai ga yin rikici a tsakanin bangarorin biyu.

Wannan ne ya sa aka kamo iyayen amarya din a ranar 6 Ga Mayu, 2018, kuma aka hada da waliyin ta.

Sai dai kuma ya ce an bada belin su a ranar 7 Ga Mayu.

Da aka tuntube shi, Abubakar Haruna, ya shaida cewa ya bada auren ‘yan mata biyu ne a rana daya.

Ya bada auren Fiddausi ga Dauda, ita kuma Saliha ga Muhammadu Murtala.

Ya ci gaba da cewa tun kafin a daure, Dauda da Muhammadu Murtala sun yi alkawarin kawo sadaki da kayan lefe kamar yadda addinin Musulunci da al’ada su ka tanadar.

“Amma ana gama shafa Fatiha sai Dauda ya ce shi fa ba zai iya kawo kayan lefe ba.

Ya ce Dauda ya harzuka har ya dauko abokan sa suka zo gidan sa suka yi masa rashin mutunci, kuma daki matar sa mai suna Bayi.

“Ba ma ta karan kan mata ta ba, har mata ‘yan biki sai da aka yi wa dukan tsiya, kuma su ka rika yin kutubal da abincin biki.

Malam Haruna ya ce ‘yan sanda karya suke yi da suka ce wai sun kama shi da matar sa da Umar Haruna Waliyin amarya saboda sun tayar da fitina.

Ya ce ‘yan sanda ba su kama wadanda suka tayar da fitina a gidan sa ba, sai ma suka ce masa wai ya biya ango N260,000 tunda amarya ta ki tarewa.

Saboda ya ce wa ‘yan sanda ba shi da wadannan makudan kudi ne suka yi masa barazanar kulle shi.

Amma Washegari da safe aka bada belin su.

A daidai lokacin da ake rubuta wannan labari, Fiddausi ta ki tarewa, ta na gidan iyayen ta.

Share.

game da Author