Jam’iyyar APC mai mulki a jihar Kaduna tayi dagadaga da jam’iyyar PDP in da ta lashe zabuka a kananan hukumi sama 14 cikin 15 da aka fadi sakamakon su.
Zaben Kaduna ta Arewa ce ake a ganin kila PDP ta tabuka wani abin azo a gani ganin cewa dantakarar jam’iyyar, wato Sabo Bababyaro sananne ne kuma mai jama’a shiko na APC ba a san shi ba, sai gashi sakamakon ya nuna cewa Sale Shuiabu na jam’iyyar APC ya yi fatafata da shi inda ko keyar sa bai hango ba.
Kusan kashi 90 bisa 100 na kuri’un da aka kada a karamar hukumar Kaduna ta Arewa, APC ce ta lashe wannan kuri’u inda PDP ko keyar ta ba ta hango ba.
APC ta lashe kananan hukumomin Kaduna ta Arewa, Birnin Gwari, Soba, Ikara, Zaria, Lere, Ikara, Makarfi, Birnin Gwari, Giwa, Kagarko, Kudan, Igabi da Kajuru.
Ita kanta karamar hukumar Makarfi da nan ne mahaifar tsohon shugaban jam’iyyar PDP ta kasa, Ahmed Makarfi, bata tsira daga goguwar APC a zaben kananan hukumomin ba domin tatas tayi a wannan karamar hukuma.