Jihar Kaduna, karkashin gwamna Nasir El-Rufai zata gudanar da zabe na farko a Kasar nan da za a yi amfani da na’ura wajen Kada kuri’a ba akwatin zabe ba.
Bayan an tantance Ka za Ka je gaban na’urar ka latsa hoton jam’iyyar da kake so nan take ka gama zabe. Sai na bayan Ka ya matso gaba.
Haka za ayi tayi har sai an gama. Daga nan sai kuma a Fara kirge. Wannan karon a gaban Ka na’urar za ta nuna maka yawan kuri’un da kowacce jam’iyya ta samu.
Jihar Kaduna dai itace wuri na biyu da za a taba amfani da wannan na’ura a nahiyar Afrika bayan kasar Namibia sannan ta shiga Cikin Jerin kasashen Duniya 10 dale amfani da irin wanann fasaha.
Da wannan na’ura babu batun an waske da akwatin zabe, ko kuma Wanda bai Kai yayi zabe ba yayi.
Shugaban hukumar zabe na Jihar Kaduna Saratu Abdu ta ce duk da sun yi hasarar wasu daga Cikin na’urorin a dalilin gobara da hukumar tayi, ta ce suna da isassun na’urori domin zaben.