Kaduna ta tsakiya sai Uba Sani, Inji El-Rufai

0

Gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai ya yi kira ga mutanen Kaduna ta tsakiya da su zabe mai ba shi shawara kan harkar siyasa Uba Sani a zaben 2019.

El-Rufai ya daga hannun Uba Sani a lokaci da ya jagoranci tawagar APC zuwa Kananan hukumomin Kajuru, chikum da Igabi wajen yin kamfen din zaben Kananan hukumomi da za a yi a Jihar ranar Asabar.

Sanata Shehu Sani ne ke wakiltar wannan yankin a majalisar Dattawa.

Yin haka da gwamna El-Rufai ya yi ya samo asali ne tun bayan rashin jituwa da ta shiga tsakanin sa da sanatoci uku dake wakiltar Jihar Kaduna a majalisar Dattawa.

Amma dai gwamna El-Rufai da Sanata Shehu Sani na su ba a ga macijin ya faru ne Jim kadan bayan rantsar da Gwamnatin APC a Jihar a 2015.

Ko da yake ba shi kadai bane dan takarar kujerar a Jam’iyyar APC, hakan ya nuna cewa sauran masu yakin neman darewa kujerar su yi ta kan su, Kenan ko kuma suyi Shirin fafatawa da zabin gwamna a zaben fidda dan takara.

Share.

game da Author