An kama masu safarar ‘Kodin’ a jihar Kwara

0

Jami’in hukumar NAFDAC na jihar Kwara Onah Ogilegwu ya bayyana cewa sun kama wasu mutane 17 dake safarar maganin Kodin a jihar.

Ya fadi haka ne da yake zantawa da manema labarai a Ilorin ranar Alhamis.

Ya ce dakarun sojin sama sun taimaka musu wajen kama mutane su 13 daga cikin su sannan sun kamasu ne tare da wasu kwayoyin sa maye.

” A ranar Asabar din da ta gabata ne muka kama wasu mutane biyu da kwalalye make da kwalaben kodin. Sannan sun ce Kaduna suka nufa da su. Sannan mun kama wasu a Ilori.

” Ina tabbatar muku cewa za mu hukunta duk wanda muka kama yana siyar da wadannan magani da gwamnati ta hana siyar wa.” Inji Onah.

Sannan ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta hanzarta kafa dokar hana siyarwa, shigowa da sarrafa wannan magani.

Share.

game da Author