An kashe jami’in diflomasiyyar Najeriya a Sudan

0

Rahotanni sun tabbatar da cewa an samu gawar wani babban jami’in diflomasiyyar Najeriya kwance a mace shame-shame cikin jini a cikin gidan sa da ke Khartoum, babban birnin kasar Sudan.

Majiya ta ce ‘yan sanda na ci gaba a binciken gano makasan babban jami’in wanda jaridar Al-Arabiya ta Sudan ta ce shi ne ma babban jami’in diflomasiyyar Najeriya a kasar.

Wasu rahotanni da aka rika yadawa a soshiyal midiya sun tabbatar da cewa an kashe shi ne ta hanyar amfani da wuka, ba harbin bindiga ba ne.

Kamfanin Dillancin Labarai na Reuters kuma ya ce ya kasa samun ko da daya daga cikin jami’an diflomasiyyar Najeriya da ke Sudan, domin jin ta bakin su.

Share.

game da Author