Ministan kiwon lafiya Isaac Adewole ya bayyana cewa gwamnati ta dauki wasu matakai domin kare yan Najeriya daga shiga turmutsitsi da hargagiyar Ebola da aka taba shi a shekarun baya.
Minista Adewale ya sanar da haka ne wa manema labarai bayan kammala za na kwamitin zartaswa a fadar shugaban kasa.
” Muna da labrin labarin bullowar cutar Ebola a kasar Kongo inda akalla mutane 17 suka rasu. Kungiyar kiwon lafiya ta duniya (WHO) da kungiyar likitocin jinkai ne sun tabbatar da bullowar cutar a kauyen Ikoko Impenge a garin Bikoro dake kasar na Kongo.”
Ya ce a dalilin haka gwamnati ta daura damarar ganin toshe duk wata kafa da cutar ka iya shigowa kasar domin kare mutanen Najeriya.
Ya kuma tabbatar da cewa gwamnati ta sami nasaran dakile yaduwar zazzabin Lassa a kasarnan tun daga watan Janairu sannan gwamnati na kokarin ganin an shawo kan yajin aikin da ma’aikatan jinya ke yi su samu su koma aikin su.
Ga matakan da gwamnati ta dauka:
1. Za a kafa wuraren gwajin cutar Ebola a duk tashoshin kasar nan.
2. Za kuma a karfafa yin gwaji a asibitocin kasar nan.
3. Hukumar hana yaduwar cututtuka na kasa (NCDC) za ta aika da ma’aikatan ta domin taya kasar Kongo shawo kan cutar.