Majalisar Tarayya za ta binciki almubazzaranci da kudaden aikin killace makarantun Arewa-maso-gabas

0

Majalisar Tarayya ta yanke shawarar binciken yadda aka yi wacaka da kudaden ciyar da dalibai na yankin Arewa-maso-gabas.

Hakan ya biyo bayan wani kudiri ne da Hon. Shuaibu Abdulrahman daga jihar Adamawa ya gabatar a zauren majalisa.

Da ya ke gabatar da kudirin, ya ce kudaden sun fito ne a matsayin tallafi ko taimako da a kira Safe ‘School Intervention Fund’ na kasashen Duniya da aka kaddamar a karkashin shugabancin tsohon Firayi Ministan Ingila, Gordon Brown, shekara hudu da ta gabata, bayan an sace dalibai mata a sakandaren Chibok.

Ya ce wasu makudan kudaden da ba a tantance yawan su ba da Najeriya ta karba da nufin kare rayukan dalibai na yankin Arewa-maso-gabas, ba a san yadda aka yi da su ba.

Kudin a cewar sa an karbo su da niyyar za a gina doguwar katanga da shingayen waya, a killace kowace makaranta, a saka musu kyamarar CCTV mai gani har hanji a kowace makaranta.

Sai dai kuma ya nuna takaicin cewa rashin gina wadannan ababe ne ya kawo sanadiyyar sace ‘yan matan Dapchi.

Ba tare da bata lokaci ba ne Kakakin Majalisa ya amince da kudirin, kuma nan take aka nada kwamitin da zai binciki kudaden da kuma abin da aka yi da su.

An umarci kwamitin ya gabatar da sakamakon binciken sa bayan makonni takwas.

Share.

game da Author