HAUWA MAINA: “Mutunci ya fi kudi”, Daga Ashafa Murnai

0

Na fara sanin Hauwa Maina tun cikin shekara ta 2000 ko kuma 2001. Tafiya da ce ta hada ni da ita, Ibrahim Mandawari, Shehu Hassan Kano har da marigayiya Balaraba Mohammed da wasu da na manta, zuwa Gombe. An karrama mu sosai a wannan tafiyar, domin har ganawa mu ka yi da mataimakin gwamnan jihar na lokacin.

Ban sake haduwa da Hauwa ba, sai da wata tafiya ta sake hada ni da ita da wasu zuwa Legas, a karkashin gayyatar Daraktan Bincike da Tattara Bayanai na Shugaban Kasa Goodluck Jonathan, a cikin Janairu, 2011. A can ma an karrama mu, domin har ganawa mu ka yi da Jonathan.

A wannan karo, ni ne na gayyace ta, saboda ana so na gayyaci wadda za ta iya yin abin da ake so ‘yar fim ta yi. Shekara 10 ban sa ta a ido ba, amma a ranar na tuna da ita.

Tun daga wannan ranar ban kara ganin Hauwa Maina ba, sai cikin 2017, amma mu na yin waya mu na gaisawa. A duk lokacin da muka gaisa za ta ce min, “Don Allah Oga Ashafa a rika haduwa ana gaisawa. Ai mutunci ya fi kudi. Idan wata sabga ta tashi a gidan ka, ka rika sanar da ni mana. Ai mutunci ya fi kudi, Abin da ka yi min ba zan taba mantawa ba, amma ka sani idan zumunci ya dore, to fa ba za a manta baya ba.

Na kan nuna wa Hauwa Maina cewa ta fahimci ni da ita kowa harkokin gaban sa sun sha masa kai. Ni ina Abuja, ita kuma ta na Kaduna, sannan ni kuma ba shiga sha’anin ‘yan fim na ke yi a yanzu ba, ballanatana mu rika haduwa a wasu taruka.

Daga baya sai na rika jin maganganu a Kaduna, sannan ita ma ta rika kira na a waya ta na shaida min cewa ta sha tsangwama saboda siyasa, don sun yi tallolin zaben wanda masu tsangwamar ta ba su so.

To a nan ina da tambaya. Don me za a tsangwami dan talla? Ta ce dole sai ka zabi wanda ta tallata ne? Wannan wane irin gidoganci ne? Ita ma talla aka ba ta. Duk duniya akwai wannan ka’idar ta talla ga jaridu, gidajen radiyo, talbijin, mujallu da ‘yan wasa da aka fi sani da ‘celebrities.’ Kai da ka tallata na ka wa ya tsangwame ka?

To yanzu dai kama daga wadanda suka rika jin haushin ta zuwa wadanda suka rika yi mata barazana, Hauwa ta tafi ta bar muku duniyar. Ku kuma sai ku fadada gidajen ku domin ku kara baza shimfidun da za ku ci gaba da yi wa duniya zaman-dirshan, zaman dimum-da’iman, daga nan har bisa Mahdi.

Ban sake haduwa da Hauwa Maina ba, sai a cikin 2017, a tashar jirgin kasa ta Kubwa, Abuja. Mu ka kuwa yi sa’a kowanen mu ya isa da jijjifin safiya, kafin lokacin shiga jirgi. Ta rika ba ni labarin irin halin da ta ke ciki dangane da auren ‘yar ta da ya gabato a lokacin. Ta ce min dalilin batun auren ne ta zo Abuja har muka hadu a filin jirgin kasa kan hanyar komawar ta Kaduna.

Maganar gaskiya na jinjina wa Hauwa jin yadda ta rika ba ni labarin irin hanyar da ta tarbiyantar da ’yar ta da za ta yi wa aure. Na ga kokarin ta matuka jin yadda ta sha gaganiyar kashe makudan kudade wajen ilmantar da yarinyar.

Irin yadda ta ke dora tawakkali ga Allah a kan dukkan al’amurra na rayuwa, na fahimci hakan ya kara mata kwarin guiwa sosai wajen kaiwa ga wasu nasarori da ta samu da kuma fuskantar wasu kalubale na rayuwa.

Ban san Hauwa ta kwanta jiyya asibiti ba, sai labarin rasuwar ta kawai na ji. Inna Lillahi Wa Inna Ilaihi Raji’un.

Kamar yadda ta sha ce min ba za ta taba mantawa da mutuncin da na yi mata ba, ni ma ba zan taba mantawa da mutuncin da ta yi min ba.

Hauwa Maina. Ina ganin mutuncin ki. Allah ya azurta bayan da ki ka bari. Allah ya bai wa iyalan ki juriyar hakurin rashin ki. Allah ya gafarta miki. Allah ya sa mutuwa hutu ce.

Share.

game da Author