Wani abin takaici da ban mamaki ya faru a kauyen Ojinato dake karamar hukumar Oji River a jihar Enugu inda wani matashi ya kashe mahaifin sa mai shekaru 83.
Wannan abu dai ya auku ne a ranar Juma’a ta dalilin sabani da suka samu a tsakaninsu.
Makwabtan wadannan mutane sun fadi cewa yaron ya kwade mahaifin na sa ne a kai da tabarya.
” Babu wanda ya san dalilin wannan sabani ko kuma dalilin daukan wannan mummunar mataki da wannan yaro ya yi” Kamar yadda suka ce.
A karshe kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Ebere Amaraizu ya ce sun kama wannan yaro sannan za su fara gudanar da bincike a kan sa nan ba da dadewa ba.
Sai dai kuma wani cikin makwabtan nasu ya bayyana cewa yana ganin kamar yaron tun da dadewa bya na da dan tabuwar hankali.