Idan ba a manta ba gwamnatin Najeriya ta dakatar da shigowa da sarrafa maganin tari da ke dauke da ‘Kodin’ da shi kan sa ‘Kodin’ din a makon da ya gabata. Sai dai ba a nan gizo ke saka ba domin kusan shi wannan ‘kodin’ din daya ne daga cikin jerin wasu kwayoyi da ake amfani dasu kaca-kaca a kasar nan wanda illar su ya fi kodin din ma.
‘Yan Najeriya sun yaba wa gwamnati kan hana siyar da wannan magani na Kodin, sai dai kuma abin da kamar wuya domin kuwa akwai wasu da suka fi wannan magani illa ga matasan Najeriya da suma ya kamata a san yadda za ayi da su wanda idan ba haka ba za ayi ci gaban mai hakan rijiya.
Ga kwayoyin:
1. Kwayar Tramadol
Tramadol magani ne da ake sha idan mutum na fama da ciwon jiki ko kuma ciwon kai mai tsanani.
Likitoci kan bada miligaram 50 zuwa 100 ga mara lafiyan dake fama da irin wannan matsalar amma idan ya fi haka yakan sa mutum maye, mutum ya rasa inda yake da yin sumbatu marasa ma’ana domin karfin maganin daidai yake da tabar wiwi.
Bayanai sun nuna cewa banda mayen da maganin ke sa wa matasa na amfani da ita domin kara karfin mazakutansu.
Likitoci su ce maganin kan sa mutum ya yi fama da matsaloli kamar su amai, jiri, bushewar makoshi, suma, haihuwar musakan yara da sauran su.
2. Kwayar Rohypnol
Mafi yawan mutane sun san shi da suna Roko, Roofies, Roche, Renfol da sauran su sannan babu shagon siyar da maganin dake kasar nan da ba a samun sa.
Ita dai wannan maganin ta na da illa matuka domin ta kan kashe wa wanda ya sha ta jiki ne dalilin da ya sa kenan ake amfani da shi wajen saka wa mata a abin sha idan za a yi lalata dasu da karfin tsiya.
Maganin kan dauki tsawon mintuna 20 zuwa 30 kafin ya fara aki a jikin mutum sannan idan ya fara aiki mutum ba zai iya sanin abin dake faruwa da shi ba kwata-kwata, ko motsa jiki ba zai iya ba.
Bayan haka maganin kan dauki mutum tsawon awowi 8 zuwa 12 kafin ya warware.
3. Alabukun
Magani ne da direbobi da masu dakon kaya suka fi amfani da ita domin samun karfin a jika.
Amma sai gashi matasa kan hada shi da hodar ibilis, tabar wiwi, giya da sauran su domin su yi maye
4. Aspirin
Maganin ciwon kai ne wannan amma yanzu ya zama abin sa maye.
Matasa kan yi amfani da wannan magani su zuba shi a lemo irin su ‘Coca- cola, Fanta, Zobo da sauran su domin a yi maye ba tare da wani ya gane abin da suke yi ba.
Likitoci sun bayyana cewa yawan amfani da maganin na gurbata zuciya da huhu sannan maganin ta fi yi wa masu fama da cututtukan hawan jini da siga (Diabetics) illa.
5. Valiu wanda Hausawa ke kira ‘Baliyan’
Magani ne wanda bai kamata ana samun shi tare da izinin likita ba amma shagunan siyar da magani da wasu mutane ke siyar da shi.
Ita dai wannan magani tana da karfi so sai domin ta fi sauran kwayoyin sa maye.
Matasa kan hadiye ta kamar kwayar fanadol ko kuma su nika su su tsira wa jikin su kamar allura.
Ana sabawa da irin wadannan magunguna saboda su kan sa mutum ya kasa rabuwa da su kwata-kwata. Idan ba asha su ba, akwai tashin hankali.