KWALERA: Za a yi wa mutane 600,000 rigakafi a jihar Bauchi

0

Kungiyar kula da kiwon lafiya ta duniya (WHO) ta bayyana cewa za ta yi wa mutane 600,000 allurar rigakafin kwelara a jihar Bauchi.

Kungiyar ta sanar da haka ne ranar Litini inda ta bayyana cewa yin haka ne mafita daga kangi ciwon kwaleran da ke sanadiyyar rayuka a kasar nan.

” Za mu yi wa mutane miliyan biyu a kasashen Afrika biyar alluran. Kasashen sun hada da Zambia, Uganda, Malawi, Sudan ta Kudu da Najeria.”

Kungiyar ta kuma kara da cewa kamfanonin sarrafa maganin allurar rigakafi ‘Gavi da Vaccine All tanaji sun isassun kudade da magungunan da za a bukata domin gudanar da wannan aiki.

” Za kuma mu hada hannu da ma’aikatan kiwon lafiya na kowace kasa da kungiyar ‘Global Task Force on Cholera Control (GTFCC)’ domin samun nasaran aikin.”

Bayan haka shugaban WHO Tedros Ghebreyesus ya ce za a yi rigakafin sau biyu ne.

Share.

game da Author