Shugaban Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres, ya yi tir da mummunan harin da wasu mahara suka kai kauyen Gwaska da ke cikin Karamar Hukumar Birnin Gwari cikin Jihar Kaduna.
A wannan hari na baya-bayan nan, mahara sun kashe akalla mutane 58, yayin da wasu kuma da dama sun samu raunuka.
A cikin jawabin da kakakin Guterres, mai suna Stephane Dujarric ta fitar, shugaban ya nemi gwamnatin Najeriya ta kamo maharan ta hukunta su daidai abin da doka ta tanadar ga irin su.
Wasu rahotanni kuma sun tabbatar da cewa wadanda suka mutu sun kai mutum 70.
Shugaban ya kuma nuna damuwar sa ganin yadda ake ta samun tashe-tashen hankula wannan shiyya.
Sai ya yi kira cewa Majalisar Dinkin Duniya za ta meni ta shiga a yi aiki tare domin a kawo karshen zubar da jinin da ake yawan yi.
Daga nan sai ya mika sakon ta’aziyyar sa ga iyakan mamatan gwamnatin Najeriya da kuma al’ummar ta gabadaya.