Tinubu ta yi kira ga gwamnati ta bada hutu domin kowa ya je ya karbi katin zabe

0

Sanata Oluremi Tinubu, wadda ke wakiltar Shiyyar Lagos ta Tsakiya, ta yi kira ga gwamnatin tarayya da ta bada hutun-game-gari a kasar nan baki daya, domin kowa ya samun damar zuwa ya yi katin rajistar yin zabe.

A wani jawabi da ta fitar a Lagos, sanatar wadda ita ce uwargidan Sanata Bola Tinubu, ta bayyana cewa katin zabe abu ne mai muhimmanci a kasar nan, kamar yadda mallakar sa ma ga kowane dan kasa da ya isa jefa kuri’a abu ne mai matukar muhimmanci.

Tinubu ta yi wannan bayani ne, jin cewa zuwa yanzu akwai katin zabe kimanin miliyan bakwai a hannun INEC, wadanda har yanzu masu su ba su je sun karba ba.

Sama da miliyan daya daga cikin su kuwa an ce na al’ummar jihar Lagos ne.

Ta ce zaben 2015 ya koya mana darasin cewa kuri’ar kowa ta na da tasiri a kasar nan.

Dalili kenan ta ke kira da bada wannan hutu, domin haka ne kawai zai sa a tsaida harkoki a ko’ina don kowa ya je ya karbi katin rajistar sa, wanda kuma bai kai ga yi ba, sai ya garzaya ya yi rajista.

A na ci gaba da rajistar katin zabe a fadin kasar nan, daga 9 na safe zuwa 3 na yamma, a wuraren da aka kebe a na yin rajistar.

Za dai a dakatar da yin rajista ne kwanaki 60 kafin a fara zabe.

Share.

game da Author