A ranar litinin ne dubban ‘yan jam’iyyar APC a jihar Kaduna suka canza sheka zuwa jam’iyyar PDP.
A bukin wanke sabbin masu canza shekar da akayi a garin Zonkwa, karamar hukumar Zangon Kataf, tsohon shugaban jam’iyyar PDP, Ahmed Makarfi ya nuna jin dadin sa ga dubban mutanen da suka canza shekar yana mai cewa, ” Da ikon Allah, Addu’o’in talakawan Kaduna Allah yaji kuma ya amsa duka.”
Sannan ya yi kira ga ‘ya’yan jam’iyyar da su tattaru su hada kai su tabbata sun kare kuri’un su a zaben kananan hukumomi da za ayi a karshen makon nan.
Shi ko shugaban jam’iyyar PDP na jihar Kaduna Hassan Hyet yabon sanatocin jihar uku yayi na kin amincewa da yi wa jihar karin bashi da aka nemi a yi. Sannan ya soki jam’iyyar APC kan rashin tsaro da ake ta fama dashi a sassan kasar nan.
Bayan haka a taron an mika wa duka ‘yan takaran shugabancin kananan hukumomin jihar na jam’iyyar tuta.