Babbar Kotun Lokoja ta dage sauraren batun bayar da belin Sanata Dino Melaye zuwa ranar Alhamis mai zuwa.
Ana tuhumar Melaye, Kabiru Seidu da Nuhu Salihu da caje-cajen laifuka har guda bakwai da suka shafi mallakar makamai, hada baki a tsakanin su su aikata laifi da kuma harkallar makamai.
Mai Shari’a Nasir Ajanah ne ya yanke hukuncin dage karar zuwa ranar Alhamis.
Ajanah, wanda shi ne Babban Cif Jojin Jihar Kogi, ya bayyana cewa dage karar zai bai wa lauyoyin da ke kare wadan ake kara su gabatar da dalilan su kwarara na neman beli.
Ya ce haka su ma masu gabatar da kara za su samu wadataccen lokaci har nan da kwanaki uku kenan yadda za su iya gabatar wa kotun hujjojin su na kin son a bayar da belin Dino Melaye.
Jagoran masu gabatar da kara, Alex Izinyon, ya roki kotun kada ta bayar da belin Dino Melaye, domin a baya an taba kama shi, amma ya kubce daga hannun jami’an tsaro ya dira daga cikin motar da ake dauke da shi zuwa kotu.
Lauyan Dino, Mike Ozekhome, ya shaida wa kotu cewa Dino ya na bukatar a bayar da belin sa ganin halin da ya ke ciki, domin abin da mai gabatar da kara ya shaida ba shi ne gaskiyar lamarin da ya sa Dino ya diro daga cikin motar ‘yan sanda ba, har ya ce ba zai yarda ya sake shiga ba.
“Ana cikin tafiya ne zuwa Lokoja ‘yan sanda suka fara fesa masa barkonon-tsohuwa, alhalin kuma ya na fama ciwon asma.”
Ozekhome ya ce Dino ya yi sauri ya diro ne a daidai lokacin da aka isa randabawul na Area 1, saboda ya na neman yadda zai yi numfashi ne afujajan a lokacin don ya ceci ran sa.