Za a yi wa matasa 133,324 masu neman aikin dan sanda gwajin kwakwalwa

0

Hukumar ’Yan sandan Najeriya, ta bayyana cewa za a yi wa kimanin matasan da ke neman shiga aikin kurtun dan sanda wadanda za a yi wa gwajin tabin-hankali sun akai 133,324.

Sanarwar ta ce wannan gwaji da za a yi musu na tilas ne.

Shugaban Muhammadu Buhari ne ya bada umarnin a dauki sabbin ‘yan sanda 6,000 a fadin kasar nan, amma ya zuwa yanzu akwai masu neman shiga har matasa 133,324.

Mataimakin Sufeto Janar na ’Yan sanda mai kula da horas da jami’ai, ya ce makasudin yin wannan gwaji shi ne don kada a cikin rashin sani a dauki rikakkun ‘yan kwaya a aikin dan sanda.

Baya ga wannan kuma ya kara da cewa za a yi musu gwajin lafiyar su domin a tabbatar da sai wanda zai iya aikin garau za a dauka.

Nyang, ya ci gaba da cewa baya ga wadannan, za a kuma tabbatar da cewa takardun kowane sun cika daidai, ya cancanta a dauke shi aikin.

Idan ba a manta ba, PREMIUM TIMES HAUSA ta ruwaito cewa daga cikin sharuddan wadanda za a dauka aiki, sai wanda ya zauna jarabawar JAMB kuma ya ci. Za a shirya musu jarabawar ne kwanan nan.

Ya yi nuni da cewa za a dauki ‘yan sandan daga dukkan fadin kasar nan, ba za a tsallake ko da karamar hukuma daya daga cikin kananan hukumomin kasar nan 774 ba.

Share.

game da Author