A sabuwar cecekuce da ya barke tsakanin sanata Sule Hunkuyi da shugaban kwamitin da ta shirya sannan ta kula zaben Kaduna na APC, Adamu Modibbo, inda dukkan su suke karyata juna cewa anyi, ba a yi ba zaben shugabannin mazabun jihar Kaduna na APC.
Modibbo ya bayyana cewa tabbas an gudanar da zabukan cikin lumana da kwanciyar hankali sannan duk wanda yayi takara ya amince da sakamakon zaben.
Yace babu inda ba ayi zaben ba sannan ya’yan jam’iyyar duk sun fito sun yi zabe.
Sai dai kuma wani hanzari ba gudu ba, Sanata Sule hunkuyi ya karyata wannan batu inda ya ce ba gaskiya bace wannan magana da Modibbo yayi.
Hunkuyi ya ce gaba daya mutanen su da suka siya wannan fom basu sami daman yin zabe ba a ko ina a jihar.
” Bayan mutanen mu sun siya wannan fom, sun garzaya rumfunan zabe amma suka tadda babu wani wakili na jam’iyyar da ya bayyana a wannan wuri.
Saboda haka mu a namu bangaren kawai ba a yi zabe a Kaduna ba.