ZABEN APC: Idan an kashe ni ku rike gwamna Ajimobi -Danmajalisar Tarayya

0

Danmajalisar Tarayya daga jihar Oyo, mai wakiltar Kananan Hukumomin Iseyin/Itesiwaju/Kajola/Iwajowa, ya zargi Gwamna Abiola Ajimobi da cewa ya na kokarin halaka shi da wasu mambobin majalisar tarayya.

Hon. Abiodun Olasupo, ya shiga shafin sa na Facebook a jiya Lahadi ya rubuta cewa. “Idan ku ji labarin cewa na mutu, an kashe ni ko an sace ni, to Gwamna Isiaka Abiola Ajimobi ne ke da hannu.’

Gwamna Ajimobi shi ne surikin gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje.

Wannan rubutu da ya yi ya janyo sharhi sosai da sosai a soshiyal midiya, musamman ma magoya bayan sa da abokan sa, wadanda suka rika neman sanin dalilin abin da ya faru. Amma dai shi bai maida wa kowa amsar abin da ya nema ba.

Yayin da PREMIUM TIMES ta tuntubi dan majalisar, ya tabbatar da cewa tabbas shi ya yi rubutn a shafin sa Facebook, kuma ya tura da kan sa. Ya ce ya yi ne saboda shi da wasu abokan sa ‘yan majalisar tarayya sun boye, saboda barazanar kashe su da ake yi.

Ya ce abin ya faru ne tun a ranar Asabar a lokacin da ake kokarin gudanar da taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC a ofishin jam’iyyar na jiha.

Ya ci gaba da cewa wani dan majalisa mai suna Akinade Fijabi da mahaifin sa sun dauko hayar ‘yan iska suka shigo da su a cikin sakateriyar APC a Ibadan, inda ake shirin yin taron.

“Kowanen su daga mai bindiga sai mai gora, sai mai adda. Haka suka shigo su ka fara harbin-kan-mai-uwa-da-wabi a sama, har jama’a da dama suka ji raununa.”

“Yanzu da na ke maka maganar nan, ba a san inda abokai na Dapo Adesina da Sunday Adepoju su ke ba.

“Shi kan sa Ministan Sadarwa (Bolaji Shittu) sai da ya dafe hular sa ya arce a guje, ya fada cikin wani ofis don kada harbi ya same shi.”

“Har ma wasu jami’an sa-ido kan zaben sai da suka ji ciwo, wasu ma sun karairaye hannaye da kafafu.’’

Ya ce duk wannan ta’addanci a kan idon Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar Oyo aka gudanar da shi.

“Ba don Allah ya sa jami’an tsaron da mu muka tafi da su daga Abuja sun fita sun fafata da ‘yan iskan ba, ai da yanzu sai dai gawarwakin mu kawai.’’

Daga nan ya kara da cewa, ko da aka watse daga wurin taron, sai gwamna ya je wurin tare da wasu mutanen da ya umari cewa wai su ne za a dora a matsayin shugabanni.

Sai dai kuma dan majalisar ya ce duk kokarin da gwamna Ajimobi ya yi domin yin karfa-karfar dora wadanda ba a so, hakan bai yiwu ba, saboda dukkan su ko fam na tsayawa takara babu wanda ya yanka.

” To mu kuma sai jami’an tsaron da muka je da su daga Abuja su ka taimaka mana da kariya, ba mu hakura ba, mu ka sake komawa sakateriyar.”

“Mu ka hana gwamna yin duk iskancin da ya so yi. A yanzu haka da na ke magana, ya umarci ‘yan takifen sa da cewa duk inda na ke su nemo ni su kashe.”

Yayin da PREMIUM TIMES ta tuntubi Danmajalisar Tarayya Fajibi, wanda Olasupo ya ce shi da uban sa sun dauki hayar ‘yan daba dauke da makamai, ya tabbatar da cewa an yi rikici a wurin, amma ba shi da hannu.

“Ni babu ruwa na, wadanda ke kokarin barin jam’iyyar ne suka haddasa wannan rikicin.

“Bari ma na fada muku, ni na tuka kai na da kai na har zuwa wurin taron. Ta yaya za a ce na ja zugar ‘yan daba kuma?”

Shi kuwa Kwamishinan ‘Yan sandan Jihar Oyo, ya bayyana wa PREMIUM TIMES cewa wani ‘‘dan sabani ne kawai ya faru a wurin. Ba tashin-hankali ba ne, sabani ne a tsakanin ‘yan jam’iya.’’

Ya kuma karyata cewa ya na wurin aka yi hatsaniyar.

Kakakin Gwamnan Jihar Oyo, mai suna Tunji, bai dauki kiraye-kirayen wayar da PREMIUM TIMES ta rika yi masa ba, kuma bai amsa sakon tes ba, ballanatana a ji ta bangaren gwamnan.

Jihar Oyo ta shiga cikin rikicin siyasa tun a 2015, inda APC a jihar ta rabu biyu – akwai bangaren gwamna, akwai kuma bangaren Minista Bolaji Shittu, wanda ke kokarin maye gurbin gwamna Ajimobi a zaben 2019.

Share.

game da Author