Fa’idojin Da Muke Amfanuwa Da Su A Duk Lokacin Da Muka yi Addu’a Muka Roki Allah, Daga Imam Murtadha Muhammad

0

Fa’idojin Da Muke Amfanuwa Da Su A Duk Lokacin Da Muka yi Addu’a Muka Roki Allah, Daga Imam Murtadha Muhammad

Bismillahir Rahmanir Rahim

Assalamu Alaikum wa rahmatullah wa bara ka tuhu

Ya ku ‘yan uwana masu daraja, mu sani, rokon Allah da addu’a suna da fa’idoji masu yawa da muke amfanuwa da su. Ga kadan daga cikin su:

1. Fa’ida ta farko: Samun lada mai yawa da sakamako mai girma a wajen Allah. Domin addu’a ibada ce daga cikin ibadu masu girma da matsayi a wurin Allah.

2. Fa’ida ta Biyu: Nisantar gafala. Domin mai addu’a yana cikin masu ambaton Allah mai yawa, domin duk lokacin da zaka roki Allah hakika kana tuna Allah ne tare da ambaton sa.

3. Fa’ida ta Uku: Samun sauki, waraka da biyan bukata a cikin dukkanin al’amuran mu. Mai yawan addu’a zai samu biyan bukatarsa a wajen Allah In Shaa Allah.

4. Fa’ida ta Hudu: Addu’a tana karawa bawa dogaro ga Allah. Sannan tana kara kusantar da bawa zuwa ga Allah.

5. Fa’ida ta Biyar: Addua tana magance masifu da bala’o’i, kuma tana canza kaddara, tare da samun kariya daga dukkanin damuwa, fitintinu da masifa ko wace iri ce.

6. Fa’ida ta Shida: Samun tsira daga fushin Allah. Domin tabbas, Allah yana fushi da wanda baya rokon sa.

7. Dukkanin mu albarkacin addu’a muke ci. Domin irin makirce-makirce da ake kullawa Musulunci da Musulmai, kuma ake kullawa kasar mu Nigeria, wallahi, da ba domin addu’a ba da yanzu babu kasar nan.

Sannan addu’a tana da karfin juya mummunar kaddara mara kyawo zuwa kyakkyawa ta alkhairi. Misali, Allah ya kaddara mutum zai yi hadari ya mutu a hanya kaza, ko wani bala’i zai afkawa mutum, sanadiyar addu’a sai Allah ya canza shi daga kaddara ta sharri zuwa kaddara ta alkhairi.

Allah ya bamu ikon rokon sa, kuma ya amsa mana dukkan addu’oin mu, ya kuma bamu ikon rokon sa da yawa, amin.

Wassalamu Alaikum

Dan uwanku:

Imam Murtadha Muhammad Gusau, daga Okene, jahar Kogi, Nigeria. +2348038289761.

Share.

game da Author