Wani jagorar jam’iyyar APC, maisuna Yusuf Ali da aka fi sani da ‘Rabagardama’ ya bayyana cewa rashin sanin ya kamata ne da cin fuska kin halartar gayyatar da sufeto janar din ‘yan sanda Ibrahim Idris yayi majalisa.
Yusuf a wata takarda da ya fitar sannan ya mka wa manema labarai a Abuja, ya ce abin da Sufeto janar yayi cin mutuncin mulkin demokradiyya ce sannan cin fuska ga majalisa.
” Wannan Abu da Sufeto janar yayi ba zai haifar da da mai ido ba ga mulkin demkradiyya da akeyi a kasar nan.
” Saboda lalacewa ma, shi kansa shugaban kasa ba iya tankwasa shi ya yi ba, domin da kansa Buhari ya fadi cewa ya bashi umarni amma ya ki yi.
” Wannan ba zance bace da za a dangantata da majalisa, wai ko ace ya shafi Saraki ne, ko mataimakinsa, EWkweremadu, wannan batu ne da ya shafi demokradiyyar kasar nan.
” Ina kira ga ‘yan Najeriya a taru a tilasta wa sufeto janar ya bayyana a majalisar, cewa ba sai a maganar kasafin kudi bane kawai za su fito su nana damuwar su. Wannan ma ya zama dole domin ceto demokradiyya a kasar nan.
Idan ba a manta ba majalisa ta gayyaci Sufeto janar din ‘yan sandan kasa ya bayyana a gabanta domin yi mata bayani kan badakalar Sanata Dino Melaye da matsalolin hare-hare da ake fama dashi a sassan jihohin kasar nan.