Mahara dauke da makamai sun babbake gidaje, sannan sun karkashe mutane masu yawa a kauyen Gwaska, dake karamar hukumar Birnin Gwari, jihar Kaduna.
Wannan abin tashin hankali ya faru ne da ranar Allah ta’ala, wato da misalin karfe biyu na rana.
Wani tsohon shugaban karamar hukumar Birnin Gwari, da baya so a fadi sunan sa ya bayyana wa PREMIUM TIMES cewa mutane da yawa ne suka rasa rayukan su a wannan hari sannan an kone gidaje masu yawa.
” Wannan abu da yake faruwa a Birnin Gwari, ya zama abin tashin hankali matuka domin kuwa ba dare ba rana. Kuma a gaskiya ‘yan sanda ba za su iya kawo karshen wannan matsala ba sai sojoji. Dole ne fa a karo yawan sojoji a wannan yanki.”
Bayan haka rahotanni sun nuna cewa maharan sun shigo wannan kauye daga garin Dansadau ne dake jihar Zamfara wanda duk bai wuce tafiyar kilomita 10 daga wannan kauye.
Wani mazaunin kauyen ya shaida mana cewa ko shi ya irga gawa sama da 20 a hanyar sa ta zuwa kafin ma ya shiga wannan kauye sannan kuma an kashe shugaban ‘yan bangan garin a hanyar sa ta shigowa shima.
Da wakilin mu ya nemi ji daga kakakin gwamnatin jihar Kaduna, Samuel Aruwan, bai dauki waya ba sannan shi kan sa kwamishinan ‘yan sanda ya yiwo tes cewa yana Coci.
Wannan abin tashin hankali dai ya zama ruwan dare a karamar hukumar Birnin Gwari.