Yadda zaben shugabannin mazabun APC ya zama taron ’yan dambe

0

Yayin da Shugaba Muhammadu Buhari ya halarci taron zaben shugabannin mazabu, wato ‘ward congress’ na jam’iyyar APC, kuma tuni har ya baro Daura, har ya yada zango a Kaduna inda ya kaddamar da jirage biyu masu saukar ungulu, jihohi da dama da aka gudanar da zabukan ba a wanye lafiya ba.

PREMIUM TIMES HAUSA ta kuma gano cewa a wasu jihohin tilas ko kuma wasu dalilai sun sa ba a gudanar da taron ba.

DELTA

A jihar Delta an burma wa wani dan takarar shugabancin karamar hukumar Ughelli wuka, kuma nan take ya mutu, aka bar shi kwance a cikin jini. Jemerier Oghaweta ya gamu da ajalin sa ne a mazabar Jeremi Ward 3, da ke Okwabe.

EKITI

A jihar Ekiti kuwa an samu rahoton afkuwar buge-buge har da rotshe a kawunan mahalarta tarukan a mazabu da dama. Wannan ya sa tilas aka dakatar da taron gangamin zaben.

RIVERS

Can a jihar Rivers kuwa Ministan Sufuri Rotimi Ameachi da Sanata Magnus Abeh, sun kwashi ‘yan kallo, yayin da suka rika surfa wa juna bakaken kalamai marasa dajin ji. Ameachi ya zargi Abbe da cewa ya nemi yin karfa-karfar dora shugabanni ba tare da yin takara ba.

EBONYI

A jihar Ebonyi kuwa, da ya ke can jam’iyyar APC ta rabu gida biyu, kowane bangare ya gudanar da na sa zaben can daban.

ENUGU

Ministan Harkokin Waje kuwa bai ji dadin yadda aka gudanar da zaben a jihar sa ta Enugu ba, dalili kenan ya yi wa zaben tofin Allah-tsine.

Da ya ke ganawa da magoya bayan sa, Minista Geoffrey Onyeama ya yi kuman cewa a yayin taron, gaba dayan jihar an maida shi da mutanen sa saniyar-ware.

BAUCHI

Rahotanni sun nuna cewa a jihar Bauchi kuwa har ofishin jam’iyya na karamar hukumar Ningi aka banka wa wuta, saboda zargin yin magudi can a tsakanin su ‘ya’yan jam’iyyar APC.

Share.

game da Author