Kotu a Ado Ekiti ta daure wani mutum dan shekara 56 da ya nemi ya yi wa wata tsohuwa yar shekara 110 fyade.
Dan sandan da ya shigar da karar Caleb Leranmo ya bayyana wa kotu cewa Benjamin ya nemi ya danne wannan tsohuwa mai shekaru 110 a gidan ta ne dake lamba 12 Igbehin a jihar Legas a ranar 30 ga watan Afrilu.
Alaklin kotun Taiwo Ajibade bayan ya saurari karan ya yanke wa Abraham Benjamin mai shekaru 56 hukuncin zama a kurkuku har sai ta kammala yin shawar da bangaren da ke Kula da irin wadannan laifuka.
Za a ci gaba da shari’ar ranar 22 ga watan Mayu.