A ranar Alhamis ne gidauniyar ‘Victims Support Fund (VSF)’ ta bayyana cewa ta ware Naira biliyan 1.6 domin gyara kananan hukumomi uku a jihar Barno.
Mataimakin shugaban gidauniyar Tijjani Tumsa ya sanar da haka a taron dankawa gwamnatin jihar Barno kudade da kayayyakin gyaran da za a bukata a garin Gwoza dake karamar hukumar Gwoza.
Kananan hukumomin da gidauniyar VSF za ta gyara sun hada da Gwoza, Mobba da Ngala a jihar Barno.
” Kudaden da muka bada tare da kayan aikin da za a bukata zai gina makarantu, asibitoci, dakunan kwanan dalibai, gidajen malamai da hedikwatar wadannan kananan hukumomin.”
” Hakan da za mu yi zai taimaka wa mutanen wadannan kananan hukumomin da suka rasa matsugunin su a sanadiyyar hare-haren Boko Haram.
A karshe, da yake mika godiyar sa ga gidauniyar gwamna Kashim Shetima ya tabbatar yi wa gidauniyar alkawarin cewa gwamnati zata yi amfani da wadannan kudade kamar yadda ya Kamata a wadannan kananan hukumomi.
Discussion about this post