Gwamnan Jihar Kaduna Nasir El-Rufai ya bayyana cewa a karon farko za a yi zabe da na’urar da zai nuna yadda ake kada kuri’a a lokacin da ake yi a Jihar Kaduna.
Wannan shine karo na farko da za ayi irin haka a Najeriya.
Shugaban jam’iyyar APC John Oyegun da wasu jiga-jigan jam’iyyar ne suka halarci kaddamar da wannan na’ura da shiri na gwamnati da akayi a Kaduna ranar Juma’a.
Gaggan APC sun halarci Kaduna ranar Juma’a ne domin kaddamar da kamfen din zabukan Kananan hukumomi da za ayi a Jihar a karshen mako mai zuwa.
” Mun kashe kudade masu yawa domin shirya wannan zabe da ganin an yi nasara. Sannan kuma wannan shine karo na farko da za a yi zabe a kasar nan da na’ura irin wannan da za mu yi amfani da shi.
” Wannan na’ura nuni ne cewa lallai muna tare da jama’a sannan kowa ya yi zabe, abin da ya zaba zai gani.
Ya ce jam’iyyar APC a Jihar Kaduna ta yi aiki tukuru don ganin ta shafe bakin cikin da PDP ta dasa a zukatan mutane.
Ya kara da cewa zuwa yanzu haka gwamnatin APC a Jihar na ayyuka sama da 1292 a fadin Jihar wanda dukkan su ana gab da kammala su.
” Gwamnatin Kaduna ta kashe sama da kashi 60 bisa 100 na kasafin kudin Jihar a fannonin inganta Ilimi da ginawa da gyara makarantu, asibitoci,hanyoyi da samar da ruwan sha.
” Mun gyara fasalin yadda ake gudanar da ayyuka a Kananan hukumomin mu yadda yanzu dukkan su na iya biyan albashi ma’aikatan su. Duk da ko mun taras da rubabbun ma’aikatan da ba a Iya biya watanni aru-aru. Yanzu duk ya zama tarihi.
Shugaban jam’iyyar APC, John Oyegun ya yaba wa gwamna El-Rufai sannan ya yi kira ga mutanen jihar da su ci gaba da mara wa jam’iyyar baya domin ci gaba da nadan romon demokradiya da gwamnan ke kwararo wa mutanen jihar.