A ranar 23 Ga Janairu, 2018, an wayi gari da rudanin wasikar da Tsohon Shugaban Kasa, Olusegun Obasanjo ya rubuta wa Shugaba Muhammadu Buhari, wadda a cikin ta ya nuna dalilan sa na cewa Buhari ya kasa yin ko da rabin abin da aka yi tsammani idan ya hau shugabancin kasar nan zai yi.
Har ila yau, babban abin da wasikar dai ta kunsa a takaice shi ne kada Buhari ya sake tsayawa takara domin idan ya yi hakan, kamar Najiriya za ta sake wasu shekaru hudu ta na tafiya da-baya-baya.
Tun daga ranar da ya rubuta wa Buhari wasika, har yau Obasanjo bai sake sassauta wa Buhari ba.
Har ta kai shi ga kafa wata kungiya mai suna Gamayyar Kungiyoyin Ceton Najeriya, wadda ake wa kallon cewa za ta rikide ta koma jam’iyyar siyasa. Ko da yake ana ganin sabuwar jam’iyyar SDP ita ce ta za kasance makamin su Obasanjo a jam’iyyance.
PREMIUM TIMES HAUSA ta dan shiga laluben dalilan da su ka sa Obasanjo ke nuna kiyayya ga gwamnatin Buhari, kamar yadda wasu rahotanni su ka nuna. Duk da irin yadda ya nuna masa goyon baya a lokacin da ake kamfe na 2015, wanda Obasanjo har kekketa katin shaidar sa na mamba na jam’iyyar PDP ya yi saboda kiyayya ga Goodluck Jonathan.
DALILAI 10 NA KIYAYYAR OBASANJO GA BUHARI
1 – Saboda an hana shi ko an ki sabunta masa lasisin mallakar rijiyar mai: Wasu rahotanni sun nuna cewa wannan ya na daya daga cikin haushin da Obasanjo ke ji.
2 – Saboda yadda Buhari ke tafiyar da gwamnatin sa: Wasikar da Obasanjo ya rubuta wa Buhari ta na dauke da wasu dalilai na rubuta wasikar. Dalilan sun hada da: rashin karfin tattalin arziki, rashin yin katabus a kan mulki, matsalar kuncin rayuwa kamar talauci da fatara, fifita wani sashe ko jinsi a kan wasu, rashin karbar laifi ko kasawa da sauran wasu dalilai.
3 – Obasanjo ya so ya jefa ‘yan-barandar sa a cikin wasu mukamai masu maiko a gwamnatin Buhari, amma aka taka masa burki. Da dama na cewa wannan dalilin ma zai iya sa huldar mutunci tsakanin dattawan guda biyu ta yanke.
4 – Wasu rahotanni sun nuna Obasanjo ya rika neman a ba shi wasu kwangilolin da aka rigaya aka bai wa wani, ko aka kebe domin wani ko wani kamfani. An ce idan ba a ba shi ba, ran sa ya rika baci sosai.
5 – Kwangilar tashar samar da hasken lantarki ta Mambilla. An ce ita ce abu na karshe da ya tunzura Obasanjo har ya rubuta wannan wasika a ranar 23 Ga Janairu, 2018.
Rahotanni sun ce Obasanjo ya so a ba wasu kamfanoni da ya nemi ya kawo wannan kwangila ta tashar samar da hasken lantarki ta Mambilla, amma aka nuna masa cewa a’a. Obasanjo ya rika kallon kan sa a matsayin daya daga cikin gaggan da suka kafa APC kan mulki, don haka duk abin da ya nema, to ya kamata a yi masa kawai.
Ya so Buhari ya yi amfani da karfin ikon sa na Shugaban Kasa, ya hana Ministan Makamashi bai wa wasu kamfanoni kwangilar domin a bai wa kamfanonin da Obasanjo ke so ya kawo, amma Buhari bai yi masa hakan ba.
PREMIUM TIMES HAUSA ta tabbatar da cewa Obasanjo ya damu da harkar kwangilar Mambilla sosai, domin a ranar 19 Ga Augusta, 2017 ya kai ziyara har wurin da za a gina tashar samar da hasken lantarkin a Mambilla. Daga wurin ya koma garin Jalingo inda har ya bayyana wa manema labarai cewa ya kai ziyara wurin ne domin kashin-kansa. “Ku ma na ga wannan wuri cewa zai yi kyau sosai da samar da harken lantarki a wurin. Don haka ya kamata a gaggauta fara aikin nan, domin idan ma ba a yi aikin nan a yanzu ba, to nan gaba tilas sai an samar da wannan tasha ta samar da hasken lantarki domin amfanin ta ga kasar nan.” Inji Obasanjo.
Gwamnatin Tarayya ta rattaba yarjejeniyar kwangilar aikin ginin Tashar Samar da Hasken Lantarki ta Mambilla a ranar 21 Ga Nuwamba, 2017. Sai ga shi Obasanjo ya rubuta wa Buhari wasikar kware wa gwamnatin sa baya a ranar 23 Ga Janairu, 2018. Wato kwanaki 61 kacal bayan da aka bada kwangilar ga Messrs China Gezhouba Corporation, Sinohydro Corporation Limited da CGOC Group Limited, a kan kudi har dala bilyan 5.792 da niyyar samar da karfin hasken lantarki har miga watts 3050.
A lokacin mulkin Shehu Shagari ne aka fara batun kafa tashar, amma hakan bai tabbata ba. Lokacin mulkin Obasanjo a 2005 kuma ya sake bada kwangilar aikin ga wani kamfanin samar da hasken lantarki na kasar Jamus mai suna Lahmeyer Hydroelectric Power. Sai dai aikin bai tabbata ba.