Lokaci yayi da za a zabi shugabannin da za su inganta kiwon lafiya a kasar nan

0

Kungiyar likitocin Najeriya ta yi kira ga ‘yan Najeriya da ‘yan siyasa cewa lokaci yayi da za a fara zaben mutane nagari da ke da kishin inganta fannin kiwon lafiyar kasar nan.

A tsokaci da ya yi a taron samun madafa a fannin, shugaban kungiyar Mike Ogirima ya koka kan yadda fannin kiwon lafiyar kasa ta gurgunce saboda nuna halin ‘ko in kula’ ga fannin da shugabanin kasar ke yi.

Ya ce kamata ya yi a sami shugabani masu kishin kasa ne da za su taimaka wajen kawar da matsalolin da ke dawo wa fannin hannun agogo baya.

” Wadannan matsaloli kuwa sun hada da mutuwan mata masu ciki, rashin isassu da kwararrun ma’aikatan kiwon lafiya, mutuwar yara kanana, yawan bullowar cututtuka, rikici, rashin ilimin zamani da sauran su.”

Ya ce yanzu da ake shirin tunkarar zabukan 2019 kamata ya yi a hada karfi da karfe a zabi shugabanin da burin su shine inganta wannan fanni a kasar nan.

A nata bayanan uwargidan shugaban majalisar dattijai Toyin Saraki, da ta halarci taron ta koka da rashin isassun kudade ne babbar matsalar da fannin kiwon lafiya ke fama dashi a kasar nan.

” Kamata yayi yadda ake ware wa fannin tsaro makudan kudade a yi wa fannin kiwon lafiya haka.”

A karshe Mike Egboh ya ce dole su hada kai a tsakanin su da ma’aikatan jinya domin ci gaban wannan fannin. sannan kuma su likitoci su guje cusa kan su a kamayamayan siyasar kasar nan.

Share.

game da Author