Jami’an tsaro da mazaunan kauyen Auno dake kilomita 24 dake gabashin Maiduguri jihar Barno sun bayyana wa PREMIUM TIMES cewa wasu mahara da ake zaton ‘yan Boko Haram ne sun kai musu hari.
Mazauna kauyen sun ce maharan sun far wa kauyen ne da karfe takwas na yammacin Laraba inda kowa da kowa ya arce daga garin.
Wani babban jami’in tsaro ya tabbatar wa PREMIUM TIMES aukuwar wannan hari sai dai ya ce bashi da cikakken bayanai kan harin.
” Bani da cikakken bayanai kan harin domin har zuwa yanzu da muke magana daku maharan na nan a kauyen Auno din.”
Discussion about this post