Duk wanda ya shuka itace daya za a biya shi N1000 – Gwamnatin Yobe

0

Gwamnatin jihar Yobe ta yi shelar cewa za ta biya Naira 1000 ga duk wanda ya shuka itace sannan ya raine ta har ta girma a fadin jihar.

Mataimakin gwamnan jihar kuma shugaban kwamitin kula da muhalli Abubakar Aliyu ya bayyana haka ranar Laraba a taron shuka itace da aka yi a kauyen Gulani dake karamar hukumar Gulani.

Aliyu yace shuka Itace zai taimakawa jihar wajen kauce wa matsalar zaizayar kasa da take fama dashi.

” Saboda haka ne muke kira ga mutane da su guji sare itatuwa, hakar ma’adinai ba tare da an bi doka ba da sauran su domin haka na lalata muhallin mu.”

Aliyu ya kuma yi kira ga kananan hukumomi, sarakunan gargajiya da su taimakawa hukumar don cimma burin ta.

Share.

game da Author