JANGWANGWAMA: ‘Yan sanda sun ciccibi Dino Melaye zuwa Lokoja

0

Kwana daya bayan ‘yan sandan Abuja sun gabatar da Sanata Dino Melaye kotu a kan gadon daukar majiyyata, a yau Alhamis kuma sun sake ciccibar sa zuwa Lokoja, inda a can ma tuni har sun gabatar da shi kotu.

A kotun da aka gurfanar da Dino ranar Laraba, an tuhume shi ne da laifin yunkurin kashe kan sa ta hanyar dirowa daga cikin motar ‘yan sanda da kuma laifin kokarin tserewa daga hannun jami’an tsaro na gwamnatin tarayya bayan an kama shi ya na hannun su.

An bayar da belin Dino Melaye a kan naira miliyan 90, a Kotun Majistare da ke Wuse Zone 2, Abuja.

Sai dai kuma dama tun a kotun, mai gabatar da kara ya bayyana wa mai shari’a cewa wannan tuhumar da ake yi masa, ba ta cikin wadda za a kai shi ya amsa ko ya kare kan sa a Lokaja, babban birnin jihar Kogi.

Dalili kenan a jiya, bayan an fito da Sanatan daga kotun ta Wuse Zone 2, saboda an bada belin sa, sai ‘yan sandan suka sake cafke shi, suka maida shi mota suka yi awon gaba da shi.

Wata sanarwa da kakakin su Jimoh Mosheed ya fitar jiya Laraba da yamma, ya bayyana cewa sun sake kama Dino ne domin garzayawa da shi Lokaja ya amsa tuhumar da kotu ke yi masa, wadda saboda kada ya je kotun ne ya diro daga motar ‘yan sanda har ya ji ciwo.

Sai dai kuma Sanata Murray Ben-Bruce ya shaida a shafin sa na tweeter a ranar Litinin cewa sanatan ya gaya masa cewa ya diro ne daga motar ‘yan sanda saboda daya daga cikin su ya fesa masa barkonon-tsohuwa a cikin ido da hanci, alhali kuma shi ya na fama da ciwon asama.

Share.

game da Author