Ma’aikatar kiwon lafiya ta kasa ta bayyana cewa bidiyon da BBC ta yi kan illolin da ke tattare da shan maganin tari da ke dauke da ‘Codeine’ ke yi wa matasan Najeriya ba shine dalilin da ya sa ma’aikatar ta dauki matakin dakatar da shigowa da sarrafa maganin ba.
Kakakin ma’aikatar Lafiya ta kasa, Olajide Oshundun ya sanar wa PREMIUM TIMES haka ranar Laraba sannan ya kara da cewa wannan matsayi da gwamnati ta dauka ya fado a kan gaba ne. Dama can gwamnati na shirin dakatar da hakan sai ga kuma wannan bidiyo na BBC da tayi.
BBC ta nuna wani bidiyo a karshen makon da ya gabata da ya nuna irin illar da maganin tare da ke dauke da ‘Codein’ ya yi wa wasu matsan Najeriya. Inda tayi tattaki zuwa wani gida da ake ajiye wadanda suka samu tabun hankali a dalilin kamuwa shan irin wadannan kwayoyi.
Olajide ya ce gwamnati ta dade da kafa kwamitin da zai duba illar wannan abu da ya addabi matasan kasar nan sannan da kuma samar mata hanyoyin da za ta bi don kawo karshen haka.
A ranar 30 ga watan Afrilu ne kwamitin ta gabatar wa gwamnati da rahoto kan binciken da ta yi da kuma shawarwarin da ya dace a dauka.
” Bayan mun karbi sakamakon,kuma mun duba ta sai muka yanke shawarar hana sarrafawa da shigo da wannan magani a kasar nan.”
Idan ba a manta ba a ranar Talata ne ministan Kiwon Lafiya Isaac Adewole ya sanar da hana shigowa da sarrafa maganin ‘Codein’ Najeriya.
Hakan ya biyo bayan illolin da aka gano maganin tari da ke dauke da codein ke yi ne wa lafiyar mutane ne.
Shaye-shayen maganin tari da ke dauke da ‘Codein’ ya zamo ruwan dare a kasar nan musamman a yankin Arewa.
An ce sinadarin da ke cikin ruwan maganin ya na da alaka da hodar iblis da kuma garin hodar a-ji-garau.
Rahotanni sun nuna cewa yawancin masu sha kwayoyi na amfani da shi idan ba su iya sayen kwayoyin buguwa masu dan Karen tsada.
Har yau dai gwamnatin jihar Katsina ba ta yi wata doka da ta haramta sha da safara da sayar da maganin na tari da mura ba.