Shugaba Muhammadu Buhari ya yi karin haske dangane da jawabin da yai cikin watan jiya a Landan, inda ya bayyana matsan Najeriya cewa akasarin su sangartattun jahilai ne.
Wannan jawabi ne da ya yi cikin wancan watan ya janyo masa tsangwama da kakkausan martani daga matasa da magidanta na kasar nan daga bangarori da dama.
A cikin wata tattaunawa ta baya-bayan nan da Buhari ya yi da Muryar Amurka, a can kasar a wannan lokaci da ya ke ziyara a kasar, shugaban ya yi karin hasken cewa:
“A Arewacin kasar nan, akasarin wadannan matasa ba su yi ilimi ba, ko kuma sun dan fara karatun amma su watsar tun kafin su yi nisa. Ba don albarkar ruwan damina da muka samu a damina biyu da ta gabata ba, ai mafi yawan su ba su da aikin yi, sai zaman-kashe-wando kawai.
“Ire-irin wadannan matasan fa ko da sun je neman kudi a jihohin kudu, dan abin da su ke samowa bai ma isar su biyan kudin haya ballantana abinci, sutura da kudin motar komawa garuruwan su bayan kammala ci-rani.” Inji Buhari.
Ya ci gaba da cewa duk kafafen yada labarai ne suka kara zuguguta maganar, musamman ma jaridun da ake bugawa a kullum, saboda su na yin yadda suka ga dama kawai.