Za mu kafa sabbin kotunan da za su yi maganin barayin kudin gwamnati -Buhari

0

Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa nan ba da dadewa ba gwamnatin sa za ta kafa sabbin kotunan da zu maida hankali ne hususan a kan shari’un wadanda suka wawuri dukiyar kasar nan.

Buhari ya kara da cewa za a bai wa kotunan karfin ikon kwace tsabar kudade da kuma kadarorin ‘yan Najeriya da aka yanke wa hukunci.

Ya ce duk wanda aka tuhuma amma ya kasa bayar da gamsasshen bayanin yadda ya tara kudaden da kuma dimbin kadarorin da ya mallaka, to za a kwace ne kawai ba wata-wata.

“Za a nemi su yi bayanin yadda suka tara dukiyoyin. Duk wanda ya kasa yin bayani kuwa, kwace dukiyar da kadarorin kawai za a yi, sannan kuma a hukunta shi.”

Haka Buhari ya bayyana a tattaunawar da ya yi da Muryar Amurka, a Birnin Washington, lokacin wannan ziyara da ya kai can.

Shugaba Buhari ya ce zai yi taka-tsantsan sosai wajen zabar irin alkalan da zai nada, sannan kuma a ba su dukkan hujjojin da ke nuna cewa wanda za su yi wa shari’a ya saci kudin. Har ma lambobin asusun ajiyar su da dukkan kadarorin da suka wawura. Sannan su kuma kafin su yanke hukunci, sai sun auna da albashi da alawus din da mutum ke karba, domin su ga shin za su ishe shi mallakar dukiyar ko kantama-kantaman gidajen da rukunin shagunan da ya gina?”

Buhari ya yi wannan furuci ne a lokacin da aka tambaye shi cewa duk da irin yaki da cin hanci da rashawa da ya ke ta yi, me ya sa har yau babu wani daga cikin gwamnatin sa da aka hukunta, ko aka tuhuma.

Buhari ya ce shi babu ruwan sa, duk wanda aka kama da laifi ya je ya kare kan sa. Idan ya kasa kuma, a hukunta shi.

Sai dai kuma ya yarda cewa har yanzu ba a yi wani abin a zo a gani ba wajen kamawa da hukunta wadanda aka samu da wawurar kudade.

Dalilin haka ne ma ya ce zai kafa sabbin kotuna na musamman domin wadanda suka ci dukiyar kasar nan.

Share.

game da Author