ZIYARAR BUHARI AMURKA: Mijina ya cancanci yabo daga ‘yan Najeriya -Inji Aisha Buhari

0

Uwargidan shugaban Kasa, Aisha Buhari ta bayyana cewa lallai maigidanta shugaban kasa Muhammadu Buhari ya cancanci yabo daga ‘yan Najeriya ganin irin rawar da ya taka a ziyarar sa kasar Amurka musamman ganawar sa da shugaban kasar Donald Trump.

Bayan haka kuma Aisha ta ce yanzu fa tana goyon bayan mijin ta 100 bisa 100 a yunkurin sake fitowa takara da ya yi a 2019. Sabanin cewa da tayi ba za ta goya masa baya ba idan har bai canza salon mulkinsa ba a wani hira da tayi da BBC.

Aisha ta fadi haka ne a shafinta ta tiwita ranar Litini.

Share.

game da Author