Jam’iyyar PDP ta bayyana rawar da Buhari ya taka a gaban Donald Trump a matsayin abin kunya ga shi kan sa da kuma Najeriya baki daya.
A cikin wani jawabi da kakakin PDP, Kola Ologbondiyan ya fitar, PREMIUM TIMES HAUSA ta tsamo wasu batutuwa guda 10 jam’iyyar ta ce Buhari ya aikata a matsayin abin kunya, da suka hada da:
Bayanin da Trump ya yi cewa Amurka ta ki zuba jari a Najeriya saboda har yanzu babu wani kwakkwaran yanayi na tattalin arziki a karkashin gwamnatin Buhari, hakan ya tabbatar da matsayin da PDP ke kallon gwamnatin Buhari a halin yanzu, cewa tayoyin motar tattalin arziki a sacce su ke, a karkashin mulkin Buhari.
“Amurka za ta rika zuba jari ne a Najeriya, amma sai idan kasar za ta yi amfani da irin yanayi da tsarin da mu ke so ta yi amfani da shi.” Inji Trump.
Abin mamaki ne yadda Buhari ya kasa jan zaren tattauna batun cinikin danyen mai da kasar Amurka, wanda shi ne ginshikin tattalin arzikin kasar nan.
An dan dora Buhari kan hanya domin ya yi magana mai muhimmanci da za ta amfani Najeriya kan batun cinikayyar danyen man fetur, amma sai Buhari ya ce, “Ni ba zan iya ce wa Amurka ga abin da za ta yi ba.
Me ya sa shi Trump ya ce Amurka ba za ta rika zuba jari a Najeriya ba, har sai kasar ta yi abin da Amurka a ce ta yi tukunna?
Trump ya tona wa Buhari asiri, yayin da ya ce a duk shekara Amurka na tallafa wa Najeriya da naira bilyan 1.
Idan an tuna, Buhari a cikin 2017 ya taba cewa Amurka ta tallafa wa Najeriya da dala milyan 500.
To ina sauran cikon kudin da Trump ya ce ana bai wa Najeriya?
Me ya sa Buhari bai ce dala milyan 500 kacal aka ba shi ba, kamar yadda ya shaida wa ‘yan Najeriya a shekarar da ta gabata?
Da Trump ya yi kakkausar magana a kan matsalar tsaro a Najeriya, maimakon Buhari ya maida masa amsa mai gamsarwa, sai ya yi shiru kawai. Daga iyar abin da ke cikin takardar jawabin da ya karanta, bai kara cewa komai ba.
Discussion about this post