2019: Yadda INEC za ta tsara jam’iyyu 68 a takardar zabe

0

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC, ta bayyana cewa samun karin yawan jam’iyyu ba zai zama wani kalubale ga sha’anin gudanar da zabe mai zuwa ba a kasar nan.

Daraktan Kula da Zabe da Sa-ido kan Jam’iyyu, Aminu Idris ne ya bayyana haka ranar Talata a Abuja, a yayin da ake wata muhawara kan “Yawan jam’iyyun siyasa da kuma ko za su kawo wa INEC matsala a lokacin zabe?”

Kungiyoyi ne guda biyu, CDD da kuma OSIWA suka hada muhawarar, ganin irin yawan da jam’iyyun da suka fito takara sun kai 68.

Idris ya kara da cewa dokar kasa ce ta ba da iznin yi wa jam’iyyu da dama rajista. Kan haka ne ya ce INEC ita aikin da ta key i shi ne ta tabbatar cewa yawan jam’iyuyun bas u zamo cika ga zaben da za a gudanar ba.

“A wasu lokuta mu kan lika tambarin kowace jam’iyya gefen sunan ta, domin masu zabe su samu damar tantancewa da tare da gaganiyar jan-lokaci ba.

“Ya zama tilas ga hukumar ta yi amfani da kuma yin taka-tsantsan da yawan takardar kuri’un da aka ba su, ganin irin yawan da jam’iyyun da za su shiga zabe ke da shi yanzu.

Share.

game da Author