ZAZZABIN LASSA: Likita ya rasa ran sa wajen duba mai dauke da cutar

0

Kwamishinan yada labarai na jihar Ebonyi John Okiyi ya bayyana wa manema labarai ranar Litini a Umuahia cewa daya daga cikin likitocin jihar ya rasa ran sa a dalilin duba wata yarinya da aka kawo asibitin tana dauke da cutar.

” Domin hana yaduwar cutar ma’aikatan kiwon lafiyar za ta gudanar da gwaji ta musamman ga ma’aikatan asibitin don gudun kada cutar ta ci gaba da yaduwa ba a sani ba.

A karshe Okiyi ya yi kira ga mutane da su kwantar da hankalin su, cewa gwamnati ta tanadi magungunan kawar da wannan cutar.

Share.

game da Author