Kwamishinan kiwon lafiya na jihar Adamawa Fatima Atiku ta karyata labaran da wasu gidajen jaridu ke yadawa cewa wai jihar ta killace wasu mutane 81 da wai ana zargin sun kamu da zazzabin Lassa a Jihar.
Fatima ta ce gwamnati bata kebe kowa ba face mutum daya sannan anaduba wasu mutane 102 saboda cudanyar da suka yi da mutumin da ya rasu sanadiyyar kamuwa da cutar.
‘‘Mun ba wadannan mutanen ne na’urar gwaji sannan muka umurce su da su hanzarta zuwa asibiti da zaran wannan abin gwaji ya nuna cewa sun kamu da zazzabi.”
” Shi wanda cutar ta yi ajalin sa ya fito ne daga jihar Taraba amma bai bukaci kula na asibiti ba sai da ya iso Yola.”
A karshe ta yi kira ga mutane cewa yayin da gwamanti ke iya kokarinta wajen dakile yaduwar cutar mutane su tabbata suna tsaftace muhalin su da killace abincin su daga bera.