Tsohon ministan babban birnin tarayya, Janar Jeremiah Useni mai ritaya ya bayyana ra’ayin sa na fitowa takarar gwamnan jihar Filato a 2019.
Useni ya fadi haka ne a ofishin jam’iyyar PDP dake garin Jos, da ya je siyan fom din neman takara.
A ganawarsa da shugaban jam’iyyar, Damishi Sango, da dandazon magoya bayan sa, Useni ya ce ya yanke shawarar haka ne domin ya dawo wa jihar Filato martabar ta da zaman lafiya mai dorewa.
Bayan haka kuma ya roki magoya bayan sa da su nisanta kansu daga tada zaune tsaya a ko ina a fadin jihar.
A karshe shugaban jam’iyyar PDP na jihar, Damishi Sango ya yi kira ga ‘yan takaran da su ka siya fom zuwa yanzu su tabbatar sun cika alkawaran da suka dauka.
Ya ce Jeremiah Useni ne na hudu cikin jerin wadanda suka sayi fom din yin takarar gwamnan jihar a inuwar jam’iyyar PDP.