Zan sake fasalin Najeriya cikin wata shida idan aka zabe ni -Atiku

0

Tsohon Shugaban Kasa Atiku Abubakar ya bayyana cewa zai sauya fasalin Najeriya a cikin watanni shida na farkon mulkin sa, matsawar aka zabe shi ya zama shugaban Najeriya a zaben 2019.

Abubakar ya yi wannan bayani jiya Laraba a lokacin da ya ke amsa tambayoyi, bayan da kammala gabatar da wata kasida a Gidan Taron Mashahurai na Duinya, Chatham House da ke Landan.

Ya kara da cewa zai kuma bai wa kowace jiha cikin jihohi 36 tsabar kudi har dala miliyan 250 domin su gina jihohi, ta yadda za su karfafa hanyoyin samun kudaden shiga na su na kan su.

Atiku, ya ci gaba da cewa bai yi mamakin Buhari ba da ya kira matasan Najeriya raggaye, saboda tun da ya tashi bai taba yin kowace irin sana’a ba, ballantana ya san zafin nema.

Da aka tambaye shi ko zai tsaya takara a matsayin indifenda ne, idan ya kasa samun tikitin jam’iyyar PDP, sai Atiku ya ce “Mu dai jira tukunna har lokacin ya zo.”

Atiku ya kara da cewa idan ya zama shugaban kasa, zai inganta Najeriya yadda duk wadanda ke zaune wasu kasashe za su yi sha’awar komawa kasar su Najeriya.

Share.

game da Author